Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gudanar Da Jana’izar Mutum 15 Da Suka Rasu A Gobarar New York


An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Jana’izar mutane 15 da suka rasu a gobarar da ta tashi a gundumar Bronx.

Daruruwan mutane daga sassa daban na gudandumar Bronx da ma New York da suka hada da Musulmi ne suka halarci sallar jana’iza.

An gudanar da jana’izar mutane 15 da suka rasu a cikin wata gobara da ta tashi a gundumar Bronx a birnin New York a makon da ya gabata wadda ta hallaka mutum 17 ciki har da yara 8.

Gwamnatin jihar New York ta ware dala miliyan 2 ta kafa gidauniyar bada diya ga wadanda wannan balai’I ya rutsa da su, mataimakin gwamnan jihar Brian Benjamin, ya samu halartan jana'izar tare da magajin garin birnin New York Eric Adams da shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa Chuck Schummer.

Daruruwan mutane daga sassa daban-daban na gudandumar Bronx da ma New York baki daya musamman Musulmi ne suka halarci sallar jana’izar ta mutum 15 jiya Lahadi a cikin yanayi mai tsananin sanyi.

Mutanen da suka halarci taron jana’izar sun bayyana matukar bakin ciki da alhini na rashin ‘yan uwan ‘yan Afrika wanda kusan dukkan su ‘yan kasar Gambia ne.

Antoni janar na New York Leticia James ta lashi takobi cewa hukumarta za ta yi iya bakin kokarinta ta tabbatar da na gurfanar da wani mai laifi a wannan gobara da ta tashi, wanda jami’ai suka ce injin dumama gida da wata kofar da ta lalace aka bar ta sake ne suka haddasa gobarar.

Mataimakin gwamnan jihar New York Brian Benjamin da ya wakilici gwamnar, yace muna tabbatar wa iyalai dake nan da ma waje cewa Bronx na cikin jihar New York kuma zamu kasance tare mu tabbatar wannan bala’I bi sake faruwa ba.

Shi ma shugaban majalisar dattawa Chuck Shummer zai yi duk iya kokarinsa a matsayi na tarayya a taimakawa iyalai, inda ya ce sun bukaci ofishin jakadancin Amurka a Gambia da ta daina aiki saboda annobar COVID-19.

Daruruwan mutane daga sassa daban-daban na gudandumar Bronx da ma New York baki daya musamman ‘yan uwa Musulmi ne suka halarci sallar jana’iza.

Magajin garin birnin New York Eric Adams, ya fara jawabinsa ne da godiya ga Amurkawa da suka taimakawa mutanen da bala’in ya rutsa da su, “ya ce ina godiya ga agajin 'yan New York da Amurkawa na tattara kayyakin jin kai suka taimakawa iyalai. Ya tabbatarwa mutanen Bronx cewa zai yi duk abin da ya kamata su kyakkyawar rauyuwa da suka cancanta.

XS
SM
MD
LG