Accessibility links

Firayim ministan riko na Libya yace Muammar Gaddafi yana shawagi tsakanin Nijar da Aljeriya da hamadar kudancin Libya yana kokarin hayar sojoji

Ana gwabza kazamin fada a birnin Sirte dake bakin teku a kasar Libya, inda sojojin gwamnatin wucin gadi suka kaddamar da wani farmakin sabo a bayan da mayaka masu biyayya ga tsohon shugaba Muammar Gaddafi suka fatattake su tun baya.

Mayakan gwamnatin wucin gadi sun fada jiya laraba cewa sun toshe mayakan Gaddafin a cikin wata unguwa guda, amma su na ci gaba da fuskantar turjiya sosai daga magoya bayan tsohon shugaban.

Gwamnatin wucin gadin ta ce kama garin Sirte zai ba ta damar ayyana kwato kasar baki daya.

Haka kuma a jiya larabar, wata jaridar larabci mai suna “Asharq al-Awsat” ta ambaci firayim ministan rikon kwarya na Libya, Mahmoud Jibril, yana fadin cewa Gaddafi yana zirga-zirga a tsakanin Jamhuriyar Nijar da Aljeriya da kuma hamadar kudancin Libya.

Mr. Jibril yace hambararren shugaban yana kokarin samo sojojin haya daga Sudan domin su taimaka masa wajen kafa kasa ‘yantacciya a kudancin kasar, ko kuma su doshi arewa domin gurgunta sabuwar gwamnatin. Yace Gaddafi yana son komowa kan karagar mulki ta hanyar yin amfani da bambance-bambancen siyasar dake tsakanin sojojin juyin juya halin da suka hambarar da shi.

Babu wata hanyar tabbatar da gaskiyar ikirarin firayim ministan na rikon kwarya na Libya.

XS
SM
MD
LG