Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kada Kuri'un Raba Gardama a Jamhuriyar Kwango


Shugaban Kwango Denis Sassou Nguessou yana kada tashi kuri'ar Brazzaville, Oktoba. 25, 2015.

Jamhuryar Kwango tayi kuri'ar raba gardama kan kwaskwarima ga tsarin mulkin kasar. Matakin da aka yi jiya Lahadi idan ya tabbata zai baiwa shugaban kasar Denis Sassou Nguesso damar takara wa'adi na uku.

Kwaskwarimar da ake kuduri zata kawarda wa'adin mulki sau biyu da aka kayyade ga masu neman shugabancin kasar, haka ma kwaskwrimar zata kwar da hana wadanda shekarunsu suka fi70 takarar shugaban kasa. Shugaba Nguesso, yanzu haka yana da shekaru 71 da haifuwa.

Ana sa ran samun sakamakon zaben wani lokaci cikin makon nan. Masu adawa d a shugaba Nguesso sunyi kira ga jama'a su kauracewa kuri'ar raba gardamar. Rahotanni daga Brazzaville babban birnin kasar suna nuna cewa mutane basu fito sosai ba.

An kashe akalla mutane hudu lokacin zanga-zangar nuna adawa da kuri'ar raba gardamar ranar Talata a babban birnin kasar.

Shugaba Nguesso yayi nasara a zabubbuka daban daban da aka yi takaddama akansu a 2002 da kuma 2009, ya mulki kasar a matakai daban daban a cikin shekaru 36 da suka wuce.

Shine shugaba na baya bayan nan da ya nemi yin tazarce duk da zanga zangar da mtanen kasar suka yi suna adawa da yunkurin yiw kundun tsarin mulkin kasar kwaskwarima.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG