Accessibility links

Mutanen garin Madagali, sun gudu sun bar gari, bayan hari dan 'yan bindigan da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kaimu a baya-bayannan.

‘Yan bindiga da ake kyautata cewa ‘yan boko haram ne sun yi diran mikiya a Kubla dake kusa da shedkwatar karamar hukumar Madagali.

Shugaban karamar hukumar Madagali, James Abawa Tarda yace “kawo yanzu an samu gawarwakin mutun hudu da ‘yan bindigan suka kashe, yayin da kuma suka kona majami’u biyu da wasu gidaje.”

Hon. James Abawa Tarda ya cigba da cewa ”sai karma zuwa da rana zamu san adadin, daga baya inda abin ya lafa zamu bi gida-gida amma yanzu mutane sun bar garin.”

Shima da yake tabbatar da harin kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Ahmadu Umaru Pintiri, ya nuna alhinisa game da hare-hare da ‘yan bindiga ke kaiwa a ‘yan kwanakin nan a yankin.

Kakakin majalisar kira yayi da ayi addu’a da kuma kira ga jama’a dasu kwantar da hankalinsu.
XS
SM
MD
LG