Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Sabon Hari a Jihar Benue


Wasu 'yan gudun hijra da suka fice daga gidajensu a jihar Benue

An kuma samun tashin hankali a jihar Benue mai fama da rikicin makiyaya da manoma, bayan da wasu mahara suka far ma karamar hukumar Logo.

Wani sabon hari da aka kai a karamar hukumar Logo da ke jihar Benue ya tarwatsa dubban mutanen yankin da dama wadanda suka fantsama zuwa jihar Nasarawa da ke makwabtaka da jihar.

Akalla mutane 16 ne suka rasa rayukansu, ciki har da wani basaraken gargajiya a cewar rahotanni.

Wata rubutacciyar sanarwa da jami’an tsaron jihar suka fitar ta nuna cewa mutum 10 ne suka rasu.

Hukumar ba da agajin gaggawa a jihar Nasarawa ta tabbatar da kwararar dubban ‘yan gudun hijra zuwa yankin jihar.

“Adadinsu ya kai kusan dubu 16, yanzun nan suna warwatse a kananan hukumomi biyu, wato Keana da Awe.” Inji shugaban hukumar ba da agaji a Nasarawa, Barrister Zakari Ali Maga.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan wani mummunan hari da aka kai a wasu kananan hukumomin jihar ta Benue, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 50 kamar yadda rahotanni ke nunawa.

Jihar ta Benue ta sha fama da rikice-rikicen da ake dangantawa da rashin jituwar makiyaya da manoma.

A baya, gwamnatin jihar ta kafa dokar hana kiwo a warwatse, lamarin da ya sha suka daga makiyaya.

Saurari rahoton wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG