Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Mayar Da Wasan Karshe Na UEFA Zuwa Portugal


Kofin UEFA
Kofin UEFA

An dage buga wasan ne a Turkiyya, bayan da Ingila ta saka kasar a jerin kasashen da ta hana matafiyansu shiga kasarta saboda karuwar cutar COVID-19.

Hukumar kwallon kafar nahiyar turai da ke shirya gasar Champions League ta UEFA, ta mayar da wasan karshe da za a buga tsakanin Chelsea da Manchestr City zuwa birnin Porto da ke kasar Portugal.

“Za a buga wasan karshe na UEFA tsakanin Manchester City da Chelsea a Estadio Do Dragao a Porto.” UEFA ta sanar a shafinta na Twitter a ranar Alhamis.

A baya an tsara za a buga wasan karshen ne a Istanbul na kasar Turkiyya a filin wasannin Olympics a Ataturk.

A ranar 29 ga watan Mayun nan za a buga wasan, wanda zai hada kungiyoyin Ingila biyu.

An dage buga wasan ne a Turkiyya, bayan da Ingila ta saka kasar a jerin kasashen da ta hana matafiyansu shiga kasarta saboda karuwar cutar COVID-19.

Hakan ya sa bayan wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki suka yi aka mayar da wasan karshen zuwa Portugal.

Yayin tattaunawar, an duba har da yiwuwar buga wasan a filin Wembley da ke Ingila, amma ba a kai ga cimma jituwa ba.

Filin wasan na Dragao na daukan sama da ‘yan kallo dubu 50, amma an kayyade cewa za a ba kowane bangaren kungiyoyin biyu gurbi dubu shida-shida.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG