Accessibility links

An Nada Sababbin Ministoci, an Kori Daya a Nigeria

  • Aliyu Mustapha

Shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria

Daya daga cikin ministocin Nigeria ya rasa aiki yayinda ake rantsarda sababbi 11

A cikin wani abin ba-zata, shugaba Goodluck Jonathan na Nigeria ya sauke ministansa na wassani a Laraba din nan, a daidai lokacinda shugaban ke rantsarda sababbin ministoci. Wasu daga cikin ministocin da suka fito daga yankin arewancin kasar sun sami manyan mukaman zama ministocin tsaro, harakokin waje, lafiya da matasa. Wakilin VOA a Abuja, Umar Faruk Musa ya kuma zanta da ministan watsa labarai Labaran Maku kan abinda ke gaban sababbin ministocin:

XS
SM
MD
LG