Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Rantsar Da Tsohon Shugaban Kasar Chadi A Matsayin Zababben Shugaban Kasar


(FILES) Chad's transitional president and presidential election candidate Mahamat Idriss Deby Itno acknowledges the crowd at the Place des Nations during final presidential election campaign rally in N'Djamena on May 4, 2024.
(FILES) Chad's transitional president and presidential election candidate Mahamat Idriss Deby Itno acknowledges the crowd at the Place des Nations during final presidential election campaign rally in N'Djamena on May 4, 2024.

A ranar Alhamis ne aka rantsar da Janar Mahamat Idriss Deby Itno, wanda ya jagoranci mulkin sojan Chadi na tsawon shekaru uku, a matsayin shugaban kasa.

Deby a hukumance ya lashe kashi 61 cikin 100 na kuri'un da aka kada a ranar 6 ga watan Mayu wanda kungiyoyi masu zaman kansu na kasa da kasa suka ce ba a yi adalci ba.

Da ake rantsar da shi, Deby ya ce ya rantse "a gaban al'ummar Chadi...domin cika manyan ayyuka da al'ummar kasar ta dora mana".

Chadian President Mahamat Idriss Deby
Chadian President Mahamat Idriss Deby

Shugabannin kasashen Afirka takwas da mambobin majalisar tsarin mulkin kasar da daruruwan baki ne suka halarci taron inda aka kaddamar da matashin mai shekaru 40, a matsayin shugaban kasa a fadar fasaha da al'adu da ke N'Djamena babban birnin kasar.

An ayyana Deby a matsayin shugaban rikon kwarya a watan Afrilun 2021 ta hannun wasu sojoji 15 bayan da 'yan tawaye suka harbe mahaifinsa, shugaban kasa Idriss Deby Itno, bayan shafe shekaru 30 yana mulki.

Chad's president Mahamat Idriss Deby Itno (Photo by Issouf SANOGO / AFP)
Chad's president Mahamat Idriss Deby Itno (Photo by Issouf SANOGO / AFP)

Rantsar da shi ya kawo karshen shekaru uku na mulkin soji a kasar mai muhimmanci ga yaki da jihadi a yankin Sahel da ke fama da rikice-rikice.

A cikin 2021, Deby ya samu amincewa cikin gaggawa daga kasashen duniya karkashin jagorancin Faransa, wadanda gwamnatocin sojoji suka kori dakarunta a shekarun baya a sauran kasashen da suka yi wa mulkin mallaka na Mali, Burkina Faso da Nijar.

Firai Minista Succes Masra, daya daga cikin masu adawa da Deby kafin ya zama firaminista, ya mika takardar murabus dinsa a ranar Larabar da ta gabata, sakamakon shan kaye da jam'iyyarsa ta yi a zaben bayan watanni hudu.

Kasashe da dama na yankin Sahel da ke fama da tashe tashen hankulan masu da'awar jihadi sun karfafa alaka da kasar Rasha bayan sun yanke hulda da Faransa.

Shugaban Rasha Vladimir Putin na cikin wadanda suka fara taya Deby murna.

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Yadda Masu Fama Da Larurar Gani Za Su Kada Kuri’a A Zaben Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG