Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Tafka Almundahana Da Kudaden Yaki Da Cutar Ebola


Kungiyar agaji ta Red Cross ta gano almundahana da aka tafka ta miliyoyin daloli lokacin yaki da cutar Ebola a wasu kasashen Afirka ta Yamma.

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa Red Cross da Red Crescent Society sunce sun gano cewa an tafka almundahana sosai a lokacin da ake yaki da cutar Ebola a Afirka ta yamma daga shekarar 2014 zuwa 2016.

A wata sanarwa da aka fitar, kungiyar agajin ta ce ta fusata da gano wannan almundahanar, sannan kuma ta sha alwashin ladabtar da duk wani jami’inta dake da hannu ciki.

Barkewar annobar Ebola ta yi sanadiyar rayukan mutane sama da dubu 11, ta kuma shafi mutane dubu 29, tare da cin zunzurutun kudi sama da Dala Miliyan 6, a lokacin da ta afkawa kasashen Guinea da Saliyo da Liberia.

A Saliyo, kungiyar Red Cross ta ce samu shaidar da ke nuna cewa akwai yiwuwar badakala tsakanin wani banki da tsohon ma’aikacinta wadda tayi sanadiyar asarar kudi har Dala Miliyan biyu da dubu ‘dari.

A Guinea kuma, ta gano aringizon biyan kudi na Dala Miliyan daya da dubu dari biyu. Kungiyar agjin tace za a kaddamar da wasu bincike har biyu a kasar.

Sai kuma Liberia, inda kungiyar ta gano farashin kayayyaki da kungiyar ke saya da kuma kudaden da ake biyan ma’aikata, an sami rarar ‘karin kudin da ta kai Dala Miliyan biyu da dubu dari bakwai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG