Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Kira Ga Musulmai Su Yi Aiki Da Darusan Da Suka Koya Lokacin Ramadan


Bayan kammala ibadar azumin watan Ramadan miliyoyin mutane sun halarci sallar idi a ko ina a fadin Najeriya.

Kamar sauran masallatai a masallacin Juma’a na unguwar Karkasara a jihar Kano, malam Ibrahim Tofa wanda ya jagorancin sallar ya gabatar da huduba.

Hudubar dai ta karkata ne kan jan hankali ga al’umar musulmi suyi riko da darrusan da suka koya a lokacin azumin ramadan.

Gabanin haka dai Malam Muhammadu Sani karkasara ya yi nasiha ga dinbin musulmin da suka hallara a masallacin idin game da tauhidi.

A sakon su na sallah ga musulmin jihar Kano, sarkin Kano Malam Muhammdu Sanusi na biyu da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, sunyi kira ne ga jama’a su ci gaba da zama lafiya da juna dama sauran mutane a rayuwar su ta yau da kullum, dai dai da koyarwar addinin musulinci.

Jama’a dai na ci gaba da taya juna murnar kammala ibadar Ramadan cikin nasara da koshin lafiya duk kuwa da tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:19 0:00

Facebook Forum

Sabbin kotunan soji a Maiduguri za su yi shari’a ga kanana da manyan sojoji

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zabarmawa, Zabuwa, Ghana

Yadda Aka Gudanar Da Wasan Zabuwa A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Ana ci gaba da muhawara a kan ko daga wane yanki na Najeriya yakamata shugaban kasar na gaba ya fito

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Aminu Saira

Aminu Saira
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Karin bayani akan Nishadi
XS
SM
MD
LG