Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarkin Kano Yayi Hawan Sallar Layya


Manyan jami'an majalisar Sarkin Kano na hawan salla.

Wani labari na cewa jami'an gwamnatin jahar Kano ba su halarci hawan sallar ba

An yi sallar Idi a Masallacin dake harabar tsohuwar Jami’ar Bayero ta Kano. Limamin Masallacin Sheikh Abubakar Jibril ya hori al’ummar Musulmi ta tsarkake niya game da ayyukan bautar Allah.

Kamar yadda kuka ji shi ma mai martaba sarkin Kano Alhaji Mahamadu Sanusi na biyu ya ja hankulan talakawa dangane da muhimmancin ilimin yara musamman ma 'ya'ya mata, sannan ya gargadi magidanta da su kyautata matan su na aure, su rika basu hakkokin su.

Ganin yadda hare-hare da kashe-kashe da yanke-yanken mutane ke dada addabar al'umma, Sarkin na Kano ya bukaci talakawa su taimaka wajen tabbatar da tsaro a kasa.

Wakilin Sashen Hausa a Kano Mahmud Ibrahim Kwari ne ya aiko da rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG