Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci gaba Da Jimamin Rasuwar Dalibin Najeriya Da Ya Kubuto Daga Ukraine


Dalibi Uzaifa Habibu Halilu Midaci
Dalibi Uzaifa Habibu Halilu Midaci

A daidai lokacin da yakin da ake yi tsakanin  Kasashen Rasha da Ukraine ke ci gaba da zama sanadin salwantar rayukan jama'a, tuni wasu miliyoyin mutane suka kubuta ta hanyar ficewa daga kasar.

A Najeriya, ana juyayin rashin wani dan kasar wanda ya rasu a gida, bayan ya samu kubutowa daga Ukraine.

Najeriya na daga cikin kasashen da suka yi hobbasa wajen kwaso mutanensu wadanda yaki ya rutsa da su, sanadiyyar mamayar da kasar Rasha ta kaddamar akan kasar Ukraine, abin da ya haifar da yaki tsakanin kasashen biyu.

Wasu daga cikin ‘yan Najeriya da suka samu kubuta daga yakin dalibai ne dake karatu a can kasar ta Ukraine.

Jihar Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya na da adadin dalibai 74 kuma duk an samu kubutar da su aka dawo da su gidajensu.

Sai dai ashe daya daga cikinsu yana tare da karin kwana inda ya rasu mako biyu bayan dawowa gida.

Dalibin Uzaifa Habibu Halilu Modaci mai karatun likitanci yana shekarar karatu ta uku yana rabin kammala karatunsa lamarin ya faru .

Honourable Habibi Halilu Modaci dan majalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Isa, shi ne mahaifin yaron, ya kuma ce bayan ya dawo daga Ukrain, sai suka shirya masa liyafar dawowa, bayan dan kwanaki kadan sai ya bayyana rashin jin dadin bakinsa wajen cin abinci, sai suka kai shi asibiti inda ba da jimawa ba ya cika.

Wannan rashin har wa yau ya jefa dalibai abokan karatun Uzaifa da ma ‘yan uwan da cikin halin juyayi.

Bashar Habibu Modaci kaninsa ne, tare suke karatu a Ukraine tare kuma suka dawo gida. Ya ce lokacin cikawarsa ne kawai ya yi saboda shi mai koshin lafiya ne.

Shugaban kungiyar daliban Sokoto a Ukraine Abduljalil Abdullahi ya shedi Marigayin da cewa Uzaifa mai hankali ne da kuma addini sannan akwai sha da karatu kuma mai son mutane.

Ita ma gwamnatin jihar Sokoto ta bakin Bello Isa Shatima, babban sakataren hukumar nemo gurabu da bayar da tallafin karatu ga ‘yan jiha wadda ta hada hannu da gwamnatin Najeriya wajen dauko yaran, ta ce ta kadu da samun labarin rasuwar Uzaifa.

Yanzu dai Uzaifa ya bar duniya kuma jama'a na ci gaba da yi wa mahaifansa da ‘yan uwa ta'aziya, yayin da abokan karatunsa ke cike da alhinin rashinsa.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00
Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG