Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Cigaba Da Kidaya Kuri'un Zaben Shugaban Kasar Amurka


Trump da Biden
Trump da Biden

Zaben Amurka na neman barin baya da kura, inda ake samun mabanbantan ra'ayoyi.

Amurkawa sun kada kuri’unsu a ranar Talata a zaben da wasu ke ganin shi ne ya fi kowane haifar da rarrabuwar kawuna a kasar, a zamanin baya-bayan nan.

Sama da Amurkawa Miliyan 100 ne suka kada kuri’unsu tun kafin ranar zabe, ta hanyar yin sammakon zabe ko kuma ta gidan waya. Cikin yanayi na fama da annobar koronabairos da fargabar yiwuwar barkewar zanga-zanga, gomman miliyoyin mutane suka kada kuri’arsu a ranar zabe.

Arthur Cohen, na daya daga cikin Amurkawan da suka fita zabe a nan birnin Washington DC.

Ya ce, “Ina da kyakkyawan fatar cewa, abubuwa za su tafi dai-dai, lura da cewa muna da tsarin dimokradiyya mai kwari a Amurka.”

Trump da Biden
Trump da Biden

Mutane sun kada kuri’unsu ne a dakunan taron jama’a, da coci-coci da kuma wannan masallaci da ke birnin Los Angeles.

Wannan mai kada kuri’ar cewa yake, “Yana da mahimmancin mu samu damar aiwatar da ‘yancinmu na kada kuri’a, saboda ta haka ne muke iya fadan ra’ayinmu domin sauya abin da ke faruwa, idan har ba ma son abin da ke faruwa, ko kuma dai mutum ya yi wani abu da zai yi tasiri.”

A cewar wata mai goyon bayan Joe Biden, ta yi zabe ne don samar da sauyi, hakazalika shi ma wannan mutumin mai suna Philip Martin da ya ce fafutukar nuna muhimmancin rayukan bakaken fata ta BLM ce ta tayar mai da tsimi.

“Cikin shekarar da ta gabata, an farga a kasarmu dangane da yadda aka mayar da hankali kan abubuwan da suka shafi rashin adalci, a yanayi na zamantakewa da kuma yadda ake kallon al’amura.”

A cewar Kevin, wannan zabe na da matukar muhimmanci, kuma dama kasar ta hau turbar gyaruwa.

Ya ce, “ni na zo na zabi Make America Great ne, wato yadda za a kara martaba Amurka . Na zo ne don na zabi wanda zai shugabanci kasarmu da kuma abin da zan iya yi wa kasata.”

Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Wasu da dama, irinsu Trace Hinson na ganin, babu haufi Amurka na tafiya dai-dai karkashin shugabancin Trump.

“Ina son yadda na ga shugaban kasa yake son Fifita Amurka akan komai. Na kuma yi imanin cewa ‘yan Republican suna kan hanya madaidaiciya.”

Sai dai ga baki irinsu Nasser Bayram, ra’ayinsa shi ne Amurka ta zama mai kyamar baki a karkashin mulkin shugaba Trump.

“Dukkanmu baki ne, abin ma da ya sa kasar nan ta daukaka kenan, idan tsarin wannan gwamnatin ya ci gaba a haka, kasar nan za ta shiga wani yanayi da ba za mu iya gyarawa ba.”

Akwai dai fargabar da wasu ke nuna cewa, duk ‘yan takarar da masu kada kuri’a ba za su amince da sakamakon zaben ba.

Megan Thomas a nan birnin Washington DC ta yi nata zaben.

Ta ce, “ina ga yana da kyau a karshe a cewa kowa ya lamunta da sakamakon, mu hada kanmu mu zama tsintsiya madaurinki daya, mu amince da sakamkon ko ta yaya ya zo mana.”

Joe Biden
Joe Biden

Ta yi wu ba za a samu cikakken sakamakon zabe ba, sai nan da wasu kwanaki ko ma makonni.

Dokokin zabe a Amurka sun banbanta daga jiha zuwa jiha, kamar yadda jami’in zabe Gary Scott na karamar hukumar Fairfax a jihar Virginia ya ce.

“Za a samu sakamakon farko a yau. Amma ba za a samu cikakken sakamakon ba saboda an ba mutane har nan da zuwa Juma’a su aiko da kuri’unsu ta gidan waya.”

A cewar Beth Jobson ta jihar Pennsylvania, abu mafi muhimmanci shi ne, a kidaya kuri’ar kowa da kowa.

“Ni addu’ata ita ce, Allah ya sa su bari a kirga kowacce kuri’a. Ba sai an kai ga tada jijiyar wuya ba. Sai mu zauna a tattauna. Saboda ni ina da ‘yan uwa da muke da mabanbantan ra’ayi, amma duk da haka ina son su.”

To wani abin tambaya anan shi ne, shin kidayar za ta tafi dai-dai, sannan shin duk jam’iyyun za su amince da sakamakon? Abin da Amurkawa da sauran kasashen duniya suke jira su gani kenan.

Ga rahoton da Mahmud Lalo ya hada muna cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:12:47 0:00

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG