Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Asibitocin Jihohi da Na Gwamnatin Tarayya Sun Kebe Wurare Domin Cutar Ebola


Ministan Kiwon Lafiyar Najeriya Onyebuchi Chukwu.

Kawo yanzu mutane hudu suka mutu sakamakon bullar cutar ebola tun daga lokacin da dan kasar Liberia ya shigo da ita kasar Najeriya

Ganin yadda cutar bata bata lokaci wajen kashe mutum yasa ta zame abun tsoro ga duk jama'ar kasar.

Gwamnatocin jihohi da na tarayya sun mike tsaye domin yaki da cutar. Tuni duk manyan asibitoci mallakar gwamnati a duk fadin kasar suka kebe wuri na musamman domin yaki da cutar. An kuma yi sa'a an samo maganin gwaji.

'Yan Najeriya suna fata ba za'a yiwa lamarin rikon sakainar kashi ba kwatankwacin yadda ake yiwa Boko Haram.

Ana samun cutar ne ta muamala da namun daji irin su gada,gwagwan biri, biri da jemaje. Muddin suna dashi mutum kuma ya taba naman su ko kashinsu ko ruwan idonsu yana iya kamuwa da cutar.

Alamomin cutar sun hada da zazzabi mai karfi wanda ke haifar da ciwon gabobi, kasala, matsanancin ciwon kai da ciwon makogwaro. Daga nan sai mutum ya shiga amai da gudawa, kuraje su baibaye jikinsa kana koda da hanta suyi dameji. Wani kuma jini ya kama malala a duk inda jikin ke da kafa wato kama daga baki, kunne, hanci da idanu.

Hanyar da ake bi domin gujewa cutar sun hada da tsaftace muhalli da yawan wanke hannu da watsa ruwan guba domin kashe kananan kwayoyin halitta da ba'a gani da idanu. Sai kuma a gujewa damkar naman dajin da ake tuhuma suna kamuwa da cutar.

Shi ma wanda ya harbu da cutar da gawarsa duk a kaurace masu inji masana harkokin kiwon lafiya.

Har yanzu ba'a samu magani mai kashe cutar ba kau daya amma dai akwai wanda ake gwadawa wanda wani ba'amarike ya samar.

Wasu matakan da kasar ke anfani dasu shi ne gwada duk wanda zai shigo kasar ta kasa ko ta sama domin kada a sake aikata 'yan gidan jiya. Haka ma kwanan nan shugaba Jonathan ya gana da gwamnoni da masu ruwa da tsaki a yaki da cutar. Su ma likitoci da sauran masana basu yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an yaki cutar.

Ga cikakken rahoton Ibrahim Ladan Ayawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:20 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG