Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ayyukan Kungiyoyin 'Yan Ta'adda Na Kara Tasiri a Afrika


Harin 'yan ta'adda a kasar Mali

Da alama kungiyoyin ‘yan ta’adda na ci gaba da kara karfin a wasu yankunan nahiyar Afirka, duk kuwa da kokarin da Amurka da kawayenta suke na ganin sun rage musu tasiri.

Bayanan, da ke cikin wani sabon rahoto da ofishin babban sifeton ma’aikatar tsaron Amurka ya fitar jiya Talata, na zuwa ne yayin da aka tilasta ma rundunar hadin gwiwa da Amurka ke jagoranta sake salo, ko kuma rage ayyukanta saboda annobar coronavirus na ratsa nahiyar.

Maimakon a ragewa kungiyoyin ‘yan ta’adda karfi, rahotan ya yi gargadin yaduwar coronavirus, na baiwa yawancinsu damar ‘kara bunkasa.

Gargadi game da juriyar kungiyar al-Qa’ida da kungiyoyin dake alaka da ISIS a Afirka ba sabon abu bane. Janar Stephen Townsend, kwamandan rundunar Amurka a Afirka, ya gargadi ‘yan Majalisun Amurka ‘yan watanni da suka gabata, cewa ire-iren kungiyoyin suna himmatuwa, kuma burinsu na karuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG