Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Fargaba Game Da Yaduwar Coronvirus A Amurka-Inji Trump


President Donald Trump da mataimakin Pence

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce Amurka ta shirywa duk wani abu da zai taso game da barkewar cutar Coronavirus, yayin da jami’an kiwon lafiyar Amurka suka bada labarin mutuwar farko sakamakon cutar.

Trump ya fada a jiya Asabar a wani taron manema labarai a fadar White House cewa matar da ta rasa ranta ta dalilin cutar, ta mutu ne a cikin dare a jihar Washington.

"Ya ce a halin yanzu muna da mutane 22 da suka kamu da cutar a nan Amurka, abin takaici, mace daya ta mutu a cikin dare. Mace ce ta kirki amma kuma ta huskanci ciwo mai hadarin gaske kana tana da shekaru hamsin da ‘yan kai, ciwonta ya yi tsanani cikin kwanaki hudu. Muna matuakr godiya ganin mutum 15 suna samun suaki ko kuma sun warke".

Yayin da yake fadin haka ya kara da cewa akwai yiwuwar samun karin labarin cutar a nan Amurka amma duk da haka babu wani abin fargaba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG