Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban jam’iyyar hamayya ta CPC a Nigeria, Prince Tony Momoh yace za’a daukaka kara a hukuncin kotun zaben shugaban Nigeria


Shugaba Goodluck Jonathan (file photo)

Shugaban na jam’iyyar hamayya ta CPC wadda Janar Muhammad Buhari Mai ritaya yayi takarar karkashin inuwarta yana mai cewa jam’iyyarsa zata daukaka kan hukuncin watsin da kotun sauraren karar zaben shugaban Nigeria tayi.Jam’iyyar ta CPC tayi zargin tafka magudi ne a zaben da aka yiwa Goodluck Jonathan da mataimakinsa Sambo.

A rahoton da wakilin Muryar Amurka Sale Shehu Ashaka, ya aikowa sashen Hausa Talata na cewa, kotun tayi watsi da karar ce bisa dalilan rashin gamsuwa da korafin wadanda ke karar. Lauyan jam’iyyar PDP dake mulkin Nigeria Sam Alex ya yaba da sakamaon shari’ar wadda yace kotun tayi Adalci.

Aika Sharhinka

XS
SM
MD
LG