Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayern Ta Lallasa Su Haaland Da Ci 3-1


Dan Wasan Bayern Lewandowski na murnar zura kwallonsa ta biyu a wasansu da Dortmund da aka tashi 3-1
Dan Wasan Bayern Lewandowski na murnar zura kwallonsa ta biyu a wasansu da Dortmund da aka tashi 3-1

A lokacin wasan, an soke kwallayen Haaland da Youssoufa Moukoko bayan da alkalin wasa ya ayyana cewa sun yi satar gida.

Dan wasan Bayern Munich Robert Lewandowski ya zura kwallaye biyu a ragar Borussia Dortmund a karawar da suka yi a wasan Super Cup na kasar Jamus.

An buga wasan ne a ranar Talata cikin wani zazzafan yanayi wanda har na’urar daukan hoto ta haska dan wasan Dortmund Erling Braut Haaland yana kira ga magoya bayansu, da su kara ihun kara masu kwarin gwiwar da suke yi.

Erling Haaland
Erling Haaland

Lewandowski ya fara zura kwallo ne cikin minti na 41 a wasan wanda aka buga a filin Iduna Park, sannan daga bisani Thomas Mueller ya kara kwallo ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Sai dai gabanin kwallon Lewandowski ta biyu, kyaftin din Dortmund Marco Reus ya farke kwallo daya a minti na 64, abin da ya kai wasan ga 2-1.

Kwallon Bayern ta uku ta zo ne cikin minti na 74, abin da ke nufin, Bayern ta lashe dukkan wasanninta shida da ta buga da Dortmund.

Marigayi Gerd Mueller
Marigayi Gerd Mueller

A lokacin wasan, an soke kwallayen Haaland da Youssoufa Moukoko bayan da alkalin wasa ya ayyana cewa sun yi satar gida.

Kungiyoyin biyu sun daura bakaken kyallaye a hannunsu a matsayin girmamawa ga fitaccen tsohon dan wasan Bayern Gerd Mueller, wanda ya rasu yana mai shekara 75.

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG