Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Ce Har Yanzu Bai Yanke Shawarar Zuwa Saudiyya Ba


Biden

Majiyoyi sun ce Biden na shirin tafiya Saudiyya, tare da tafiya Turai da ma Isra'ila a karshen watan Yuni.

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce "har yanzu" bai yanke shawarar ko zai tafi Saudiyya ba, mako guda bayan da bayyana yiwuwar yiwuwar yin bulaguro.

Majiyoyi sun ce Biden na shirin tafiya Saudiyya, daga nan ya wuce Turai da Isra'ila a karshen watan Yuni.

Fadar White House ta White House ta ce shugaban kasar yana jin cewa Yarima mai jiran gado na Saudiyya, Mohammed bin Salman, "baya bin doka” saboda rawar da ya taka wajen kisan dan jaridar Washington Post, Jamal Khashoggi, a Turkiyya a shekarar 2018.

Idan ba a manta ba, a shekarar 2018 ne Majalisar Dattawan Amurka ta dauki wani irin matakin da ba ta taba daukawa ba kan kasar Saudiyya, kawar Amurka ta kud-da-kud, bayan da ta amince da wani kuduri na kawo karshen goyon bayan da Amurka ke bai wa Masarautar Saudi don yin Allah wadai da kashe Jamal Khashoggi.

XS
SM
MD
LG