Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Brazil Ta Zama Ta Biyu A Yawan Mace Macen Coronavirus A Duniya


shugaban Brazil Jair Bolsonaro,

Kasar Brazil a jiya Asabar ta zo matsayi na biyu a duniya na yawan mace macen coronavirus da mutum dubu dari bayan Amurka, wacce take ta farko da mutum sama da dubu 161 da suka mutu da cutar wacce take kuma da kusan mutum miliyan biyar da aka tabbatar da sun kamu da cutar.

Ajiya Asabar kuma Brazil ta sanar da mutum miliyan uku ne aka tabbatar da sun kamu da cutar a kasar.

Shugaban Brazil Jair Bolsonaro ya fada a ranar Alhamis cewa yana cikin hayyacin sa, duk da karuwan adadin cutar. Bolsonaro shima ya tsallaka rijiya da baya a lokacin da ya kamu da COVID-19 a watan da ya gabata kuma ya ce ya yi iya kokarin sa ya ceto rayuwar mutane. Saboda rashin yawan gwaje-gwaje, masana sun ce adadin wadanda suka kamu da cutar a Brazil ka iya ninkawa sau shida.

Mutum sama da dubu daya suke mutuwa da coronavirus a duk rana ta Allah a kasar Brazil a cikin makwanni da dama, wani lamari da Amurka ta taba huskanta a cikin kwanaki 11. Brazil da Amurka suna adadi makusanta wurin yawan mace mace tsakanin mutum miliyan daya, wanda Brazil keda 478 kana Amurka keda 487. Amma kasashen biyu suna kasa da kasar Spain da kuma Italiya wadanda keda mutuwar mutum 609 da 583 tsakanin mutum miliyan daya.

Tasirin annobar ya bambanta a fadin jihohin Brazil 27. A Brasilia babban birnin kasar, kusan kashi tamanin cikin dari na asibitocin kula da masu cutar sun cika makil da jama’a, amma a Rio De Janeiro lamarin ya yi kasa da kashi talatin cikin dari. A nan Rio, shagogi da wuraren cin abinci na ci gaba da aiki kana wuraren shakatawa na gabar teku kuma suna aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG