Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bude Gidan Rawa A Saudiya Ya Huskanci Koma Baya


Yarima Mohammed bin Salman na Saudi Arabia

Jami’ai a Saudi Arabia sun ce basu amince da bude gidan rawa da aka ce an bude da yammacin ranar Alhamis a Jeddah, birni mafi girma na biyu a Saudiya.

Ana kallon Jeddah a matsayin birnin hadin gambiza ba kamar babban birnin kasar Riyadh inda ake sa ido sosai a kan dokokin mata da maza da basu da aure.

Rahotannin kafafen yada labarai sun ce wani shahararren kamfanin gidan rawa a Gabas ta Tsakiya da ake kira "White" ya bude reshe a Jeddah a ranar Alhamis amma ba a sayar da giya a wurin domin kiyaye dokokin Musuluncin kasar.

Bayan wasu sa’o’I, hukumar kula da harkokin nishadi ta kasar ta musanta cewa bata bada izinin bude gidan rawar ba. A wata sanarwar da ta kafe a shafinta na Twitter, hukumar nishadi ta Saudiya ta sanar da bude wani bincike nan da nan a kan wani hoton bidiyo da ake yadawa a kan yanar gizo da ya nuna shugabannin kamfanin gidan rawa a cikin gidan.

Sai dai ba a iya tantance sahihancin bidiyon kai tsaye ba.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG