Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NOA Ta Nemi 'Yan Najeriya Su Ba Da Hadin Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro


Garba Abari, Darektar Hukumar NOA (Hoto: Twitter Garba Abari)
Garba Abari, Darektar Hukumar NOA (Hoto: Twitter Garba Abari)

A wani bangare na taimakawa gwamnatin Najeriya shawo kan tarin mastalolin da suka addabi kasar musamman a fannin tsaro, hukumar wayar da kan al’umma ta kasa wato National Orientation Agency ta kaddamar da wani sabon kamfe.

Sabon kamfen din da zai mai da hankali wajen wayar da kan al’umma kan manyan laifuffuka da ke barazana ga zaman lafiyar kasar wadanda suka hada da bangaren siyasa, satar mutane don karbar kudin fansa da shan miyagun kwayoyi da dai sauransu.

Hukumar wayar da kan al’umma a Najeriya ta yi wa taken taron kaddamar da kamfe din kan‘’Samar Da Najeriya Mai Cike Da Tsaro Da Kwanciyar Hankali’’ a wani mataki na dakile tarin matsalolin rashin tsaro da kasar ke fuskanta.

Dakta Garba Abari, babban shugaban hukumar, ya ce daya daga cikin abin da ke tayar masu da hankali a matsayin ‘yan kasan shi ne tashi-tashen hankali, garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, rushe-rushe na kayan gwamnati da dai duk dai abubuwan da suke nuna rashin kyakkyawan tsaro a kasar.

An dai yi Allah wadai kan ire-iren laifufuka da ake aikatawa a kasar musamman ta’ammali da miyagun kwayoyi da ke zama jigon abun da ke kawar hankalin matasa har ya jefa su aikata manya laifuffuka, lamarin da ke dawo da hanun agogo baya ta fuskar tsaro.

An kuma bukaci al’umma daga dukkan bangarori da su ba da gudumowarsu wajen magance matsalar kamar yadda Esther Apo mataimakiya daraktar yada labaru da gudanar da shirye-shirye a hukumar ta fada.

Hukumar NOA a takaice tare da hadin gwiwar hukumomin tsaro da shugabanni gargajiya da wasu kungiyoyin fararen hula da sauran masu ruwa da tsaki na da tabbacin cewa wannan yunkuri zai taimaka wajen samar da yanayi na zaman lafiya, la’akari da babban zaben kasar da ke tafe a shekarar 2023.

Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

NOA Ta Nemi 'Yan Najeriya Su Ba Da Hadin Kai Wajen Magance Matsalar Tsaro
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00


XS
SM
MD
LG