Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burtaniya Ta Ba Da Rahoton Bullar Cutar Kyandar Biri Guda 104, Akasari Maza


Gwajin kyandar biri

Jami’an kiwon lafiya na Biritaniya sun sake gano wasu karin mutane 104 da suka kamu da cutar kyandar biri a Ingila a wani lamari da ya zama bullar cutar mafi girma.

Hukumar Kula da Lafiya ta Burtaniya ta bayyana a yau litinin cewa wadanda su ka kamu da cutar kyandar birin sun kai 470 a duk fadin kasar, wanda akasarin su maza ne masu luwadi. Masana kimiyya sun yi gargadin cewa kowa, ba tare da la’akari da yanayin jinsin shi ba, na iya kamuwa da cutar kyandar biri idan yana kusa, ko mu’amala da mai cutar ko ta hanyar tufafinsa ko kayan gadonsa.

Bisa bayanan Burtaniya, kashi 99% na masu kamuwar ya zuwa yanzu maza ne kuma yawancin suna cikin Landan.

A watan Mayu, wani babban mai ba da shawara ga Hukumar Lafiya ta Duniya ya ce maiyuwa barkewar cutar kyandar biri a Turai da sauean kasanshen duniya na yaduwa ne ta hanyar jima'i a wasu tarukan shakatawa biyu na baya-bayan nan a Spain da Belgium.

A makon da ya gabata, WHO ta ce an samu bullar cutar 1,285 daga kasashe 28 da ba a san su da kamuwa da cutar kyandar biri ba. Ba a sami rahoton mace-mace a wajen Afirka ba. Bayan Burtaniya, an ba da rahoton adadin mafi girma a Spain, Jamus da Canada.

A halin da ake ciki, kasashe a Afirka sun ba da rahoton mutane sama da 1,500 da ake tsammani sun harbu da cutar da suka hada da mutuwar mutane 72 daga kasashe takwas.

XS
SM
MD
LG