Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Burundi: Jam'iyyar Gwamnati Ta Gamsu da Zaben 'Yan Majalisa


Burundi: mutane sun yi layin kada kuri'unsu

Jam’iyyar dake mulki a kasar Burundi ta ce ta yi murna da yadda jama’a su ka fito wajen zaben ‘yan majalisar kasar, duk da kin fitowa da ‘yan adawa suka yi da kuma suka daga kasashen waje.

Mr. Pascal Nyabenda, shugaban jam’iyyar CNDD-FDD mai mulki, ya ce masu jefa kuria a Burundi sun yi watsi da kiran da ‘yan adawa suka yi na kin fita zaben saboda sun fi son dimokradiyya fiye da juyin mulki.

Ba ‘a sami mutane da yawa sosai ba a zaben na ranar litinin, kuma sakatare-Janar din Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon, wanda ya yi kiran a dage zaben, a jiya Litinin ya bayyana damuwa sosai akan kuri’ar da aka yi.

Jami’an zabe sun fadi cewa an kada kuri’a ba tare da wata matsala ba kafin a rufe zaben da maraice. Amma mazauna Bujumbura sun ce sun ji harbe-harben bindiga da kuma tashin nakiya akalla guda daya a babban birnin kasar, duk da tsaurarran matakan tsaro da aka sa. Amma babu dai labarin jikkata.

Ga masu suka da su ka ce zaben bai yi kyau ba, Nyabenda yace, ai wakilai daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma Kenya na wajen.

Shugabar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini Zuma ta bayyana damuwarta akan abinda ta kira matsalar tsaro da siyasa a Burundi. Sai dai masu sa ido daga tarayyar ta Afika basu halarci zaben na ranar litinin ba.

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG