Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Son Amurka Ta Soke Cinikin Makamai Da Taiwan


Hong Kong China
Hong Kong China

Kasar China ta nuna rashin jin dadinta kan shirin da Amurka ke yi na sayar wa da Taiwan makamai har na kudi Dala biliyan 1.42.

A wani mataki na ci gaba da adawa da hukumomin Taiwan, china ta yi kira ga Amurka da kada ta hhada huldar sayar da makamai da yankin Taiwan.

Gwamnatin kasar Sin din dai na son Amurka ta soke wannan ciniki, wanda ta kira a matsayin wani abin da bai kamata ba.

Ofishin jakadancin China a nan birnin Washington DC ya ce “Abin da Amurka ta yi bai kamata ba, kuma ya sabawa yarjejeniyar da shugabannin kasashen biyu suka kulla a gidan shugaba Donald Trump na Mar-a-Lago, zai kuma kawo tsaiko ga ci gaban da ake samu na dangartakar China da Amurka.”

A jiya Alhamis ne gwamnatin shugaba Trump ta sanar da ‘yan majalisun Amurka game da wannan ciniki, a cewar wata mace mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert.

China dai har yanzu tana daukar Taiwan a matsayin wani yankinta.

Cinikin dai ya zo a dai dai lokacin da ake zaman dardar, kan dangantakar dake tsakanin Washington da Beijing, a kokarin samar da hanyar shawo kan barazanar Korea ta arewa kan shirinta na mallakar makamin nukiliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG