Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Ta Soki Maganar Da Trump Ya Yi Da Shugabar Taiwan


Shugabar Taiwan Tsai Ing-wen

Yau Asabar China ta nuna korafinta kan ganawa ta wayar talho da shugaban Amurka mai jiran-gado Donald Trump ya yi da shugabar Taiwan.

Trump dai ya yi biris da tsarin dimplomasiyyan da aka kwashe kusan shekaru 40 Amurka na tafiya akansa a ranar Juma’a, inda ya tsallake China ya kira shugabar Taiwan Tsai Ing-wen.

Tun a shekarar 1979, Amurka ta yanke huldar diplomasiyya da Taiwan.

Ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya ce ya na fatan wannan ganawa ta waya da Trump ya yi da Taiwan, ba za ta janyo cikas a huldar diplomasiyyar dake tsakanin China da Amurka ba.

“Ya kamata a san cewa kasar China kasa ce daya, kuma Taiwan wani yanki ne na kasar China.” In ji ministan harkokin wajen China.

Amma daga baya ya kwatanta lamarin a matsayin wata dabarar siyasa da Taiwan ta nuna.

Trump dai ya sha suka dangane da kiran shugabar ta Taiwan da ya yi, amma a wani sakon twitter da ya aike, Trump ya ce shugabar ta kira shi ne ta taya shi murna samun nasara a zabe.

A martanin da ta mayar, Fadar White House ta ce har yanzu tana kallon China ne a matsayin kasa guda.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG