Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Da Biden Sun Ci Gaba Da Caccakar Juna Kan Rigakafin COVID-19


Trump and Biden

Yayainda Amurka da Manyan kasashen duniya ke rige-rigen samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 don kawar da annobar a doran kasa, al'amarin ya zama abin sukar juna tsakanin yan takarar shugabancin Amurka gabanin zaben na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Shugaban Amurka Donald Trump da tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Bide, sun ci gaba da caccakar juna akan riga kafin cutar COVID-19, a jawabansu daban-daban na bikin ranar ma’aikata.

A jiya Litinin Trump ya yi ikirarin cewa dan takarar jam’iyyar Demokrat Joe Biden da Kamala Harris “su hanzarta neman afuwa saboda kalamai da suka yi na nuna kin jinin rigakafi.

Biden ya bayyana a jiya Litinin cewa, yana son ya ga allurar riga kafin gobe, ko da kuwa hakan zai zama sanadiyyar ya fadi zabe. Amma “Idan ma muka sami rigakafin mai inganci, mutane ba za su yarda da ita ba” saboda jawaban da shugaban kasa ya yi ta nanatawa masu cike da kura-kurai da karairayi game da kwayar cutar sun cirewa jama’a kwarin guiwa.

Biden ya ce ya sha fadar abubuwa da dama da ba gaskiya ba ne.

Trump a lokacin da ya gudanar da taron manema labarai na farko a North Portico da ke fadar White House, ya ce sabanin “karairayin siyasa,” duk wata rigakafi da gwamantin tarayya ta amince da ita za ta kasance mai matukar sahihanci da aiki sosai.”

‘Yan takarar jam’iyyar Refublikan da na Demokrat sun yi jawaban nasu yayin da yakin neman zaben shugaban kasa ya soma kankama a hutun ranar ma’aikata na shekara-shekara, a lokacin da cutar COVID-19, da coronavirus ke haddasawa, ta ke ci gaba da kashe kusan Amurkawa 1,000 a kowace rana, a cewar wata kididdiga daga cibiyar dakile cuttuka masu yaduwa ta Amurka.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG