Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus Ta Shiga Fadar White House Ta Shugaban Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump

A jiya litinin Fadar White House ta sanar da cewa mai bawa shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Robert O’Brien ya kamu da COVID-19.

O’Brien, wanda ke jagorantar shugabantar kwamitin tsaro na Amurka, “Ya nuna alamomin kadan kuma ya killace kansa, kana yana aiki daga wani wuri kebabbe. Babu alamun hadarin na kamuwa ga shugaban kasa ko mataimakinsa,” a cewar wata sanarwa da fadar White House ta fitar.

Sanarwar ta kara da cewa aikin kwamitin tsaro na Amurka ya cigaba ba tare da tangarda ba.

O’Brien dan shekara 54, shi ne babban jami’i a gwamnatin shugaban kasa Doald Trump da aka tabbatar da ya harbu da cutar coronavirus.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG