Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Sankarau Na Ci Gaba Da Hallaka Jama'a A Najeriya Da Makwabtan Ta


Mutane sama da 260 ne suka mutu a Najeriya sakamakon cutar sankarau cibiyar kare cututtuka ta kasar ce tace kusan mutane dubu 2 ne ake kyautata zaton sun kamu da cutar ta sankarau a cikin wannan shekarar.

Shugaban cibiyar Chikwe Ihekweazu, yace anyi ta kokarin ganin ann kare yaduwar cutar amma lamarin ya ta’azzara sakamakon rashin wadatattun allluran riga kafi wanda ake fama dashi duk fadin duniya.

Sai dai yanzu haka hukumar lafiya ta duniya wadda ke da wannan rigakafin ta bada na akalla mutane dubu dari 5 wanda kuma daga watan gobe ne za a fara anfani dasu.

Cutar ta sankarau wanda ke yaduwa ta kwayar cutar halittan nan da ba a iya gani da ido yana yi wa fatar dake saman kwakwalwa illa ne, wanda yake haddasa kunburin gadon baya.

Kashi na biyu na wannan cutar kuma wanda yafi yawa a kasahen yammacin Africa, ciki ko har da Najeriya yana haifar da matsananciyar mura, ciwon kai, zazzabi, bushewar makoshi, Amai, wanda ke kunbura wani sashe na jiki.

Ita dai wannan cutar ana daukar ta ne ta iska, a kwayar halittar da ba a gani da ido, kuma takan shafi abinda keda da alaka da numfashi.

Najeriya dai na cikin bangaren kasashen Africa, dake fama da wannan cutar saboda irin yanayin ta.

Yanzu dai mutane sama da dubu 13, da dari 7 suka kamu da cutar kuma sama da dubu daya sun mutu a makwabciyar Najeriyar, wato jamhuriyar Niger, wannan kuma ya faru ne a cikin shekarar 2015.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG