Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Hadin Gwiwa Sun Kwato Wani Muhimmin Gari a Somalia


Wani wuri da mayakan al shabab suka kai harin kunar bakin wake a Somalia

Kasa da mako guda bayan da wani babban kwamandan kungiyar Al Shabab ya mika wuya ga gwamnatin kasar Somalia, dakarun hadaka sun kwato wani muhimmin gari daga mayakan.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na tarayyar Afirka tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Somalia, sun yi nasarar kwato garin Bariire da ke kudancin Somalia daga hanun mayakan Al Shabab.

Jami’an gwamnati da wadanda suka shaida lamarin ne suka tabbatar da kwato garin wanda ke da muhimmanci ta fuskar tsare-tsaren ayyukan soji.

Kwamandoji sun ce mayakan Al shabab sun fice daga garin ne bayan wani mummunan ba-ta-kashi da aka yi, inda dakarun hadin gwiwar suka tunkari garin ta fuskoki uku.

Garin Bariire, ya kasance babbar tunga ce ga mayakan na Al Shabab a yankin kudancin kasar, wanda ke da tazarar tafiyar kilomita 45 daga Mogadishu, babban birnin kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG