Dakarun kasar Iraqi suna bi taku-bayan taku, kuma gida-gida suna fafatawa da ragowar mayakan sa-kai na ISIS a Mosul, duk da cewa tuni jami'an kasar suke murnar samun nasara.
Sojojin sun bayyana cewa fadan na yanzu shine mafi tsanani a gwabzawar da suke yi da mayakan sa-kai na ISIS, inda suke shiga gidajen da mayakan suke buya suna kuma sanye da farmalolin da aka dasawa nakiyoyi.
A daidai lokacin da rana take faduwa a jiya lahadi, rahotannin sun ce jerin gwanon motocin Firai ministan kasar Haider al-Abadi suke barin "birnin Mosul da aka 'yanto."
Wasu mazauna birnin da suke cike da murna sun hallara domin karrama ziyarar tasa, tare da daukan hotuna da wayarsu ta hanu.
Facebook Forum