Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Nijar Sun Kashe Mayakan ISWAP 10 A Kan Iyakar Nijar Da Najeriya


Dakarun Nijar
Dakarun Nijar

Samun wannan galaba na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa a wasu kasashen yankin Sahel ke zargin mahukunta da gazawa a fannin samar da tsaro.

Hukumomin a Jamhuriyar Nijar sun yi ikirarin cewa dakarun kasar sun fatattaki mayakan kungiyar ISWAP lokacin da suka kai hari a sansanin sojan Chetima Wango dake jihar Diffa kusa da iyakar Nijar da Najeriya.

A wata sanarwar da aka bayar mai dauke da sa hannun ministan tsaron kasa Alkassoum Indatou, ma’aikatar tsaron Nijar ta ce wani ayarin motoci 7 dauke da mayakan kungiyar ISWAP da suka tsallako daga Najeriya ya kai hari akan sojojin dake da sansani a kauyen Chetima Wangou na yankin Diffa.

Harin a cewar sanarwar an kai shi ne da misalin karfe 7:30 na safiyar Asabar 29 ga watan Janairu, martanin da askrawan na Nijar suka mayar ya ba su damar hallaka mutun 10 daga cikin maharan tare ragargaza masu motoci uku.

A cewar hukumomin kasar, akwai wadanda suka tsira da sauransu suka gudu suka bar mota daya sakamakon wuyar da suka sha.

Samun wannan galaba na zuwa ne a daidai lokacin da talakawa a wasu kasashen yankin Sahel ke zargin mahukunta da gazawa wajen shawo kan matsalolin abin a yaba ne in ji editan jaridar la Roue de l’histoire Ibrahim Moussa magatakarda a kungiyar ‘yan jarida mai kula da sha’anin tsaro.

Sanarwar hukumomin tsaron ta kara da cewa ba wanda ya ji rauni a bangaren sojojin Nijar ballantana asarar rai , a cewar wani mai bin diddigin sha’anin tsaro a yankin Tafkin Chadi Kaka Touda Goni wannan alama ce dake nuna kwarewar dakarun Nijar a fannin yakin sunkuru.

Wasu majiyoyi sun ayyana cewa gagarumin farmakin da sojan saman Najeriya suka kaddamar a ‘yan kwanakin nan a yankin arewa maso gabashin kasar ne ya tilastwa ‘yan ta’addan kungiyar ISWAP gudowa Nijar da nufin samun mafaka a wani lokacin da ruwan Kogin Komadugu ya fara janyewa.

Sannan an yi katari matakan da Najeriya ta dauka na zuwa a wani lokacin da Jamhuriyar Nijar ta tsaurara matakan sama da kasa a yankin kudu maso gabashin kasar .

XS
SM
MD
LG