Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Aka Rufe Babban Asibitin Khalifa Isiaku Rabiu A Kano


Khalifa Isiaku Rabiu Peatrics Hospital Kano.
Khalifa Isiaku Rabiu Peatrics Hospital Kano.

Gwamnatin jihar Kano ta rufe ayyukan babban asibitin yara dake kan titin gidan Zoo a Kano shekaru uku bayan asibitin ya fara aiki.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomin lafiya a jihar suka tabbatar da cewa, fiye da mutum dubu uku sun kamu da cutar kwalara a sassan jihar.

Daya daga cikin ragowar iyayen yaran dake kwance a wannan asibitin yara na Kano suna kwance galibin a dakuna da ofisoshin dake cikin suka zama tamkar kushewa.

A lokacin da muka ziyarci asibitin kalilan ma’aikatan dake ciki sun yi jungun-jungun suna tunanin makomar rayuwa.

Wata odar kotu ce dai ta umarci kamfanin dake kula da ayyukan wannan asibiti mai suna Northfield Health Services ya kauce daga asibitin tare da ma’aikatansa baki daya, kamar yadda daya daga cikin manyan Jami’an asibitin wanda ke muradin a sakaya sunansa Ya tabbatar mana.

Karin bayani akan: Kano, Nigeria, da Najeriya.

"Mun samu umarnin kotu, cewa wadanda suke kwamitin shugabancin asibitin sun kai wadanda suke gudanar da ayyukan asibitin kotu. saboda haka ta ba da umarnin a dakatar da ayyuka."

Dr. Nasiru Kabo dake zaman sakataren zartarwa na hukumar kula da asibitocin jihar Kano ya ce ba a rufe asibitin ba, amma gwamnatin Kano ta janye yarjejeniyar kawancen aiki tsakanin ta da da kamfanin.

A shekara ta 2018 ne Asibitin yaran na Kano mai yawan gadaje 200 da ake yi wa lakabi da Khalifa Isiaku Rabiu Pediatrics Hospital, ya fara aiki karkashin tsarin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Kano da wannan kamfani na Northfield bisa wasu ka’idoji da sharruda da bangarorin biyu suka aminta da su.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakin daraktan kula da ayyukan lafiya ta jihar Kano Dr. Bashir Lawan ya tabbatar da cewa, fiye da mutane dubu 3 ne suka kamu da cutar kwalara a jihar cikin kusan watanni uku da suka gabata.

"Amma Allah da hikimarsa da sahalewarsa, ya sa mun samu damar warkar da mutum 2,996."

Saurari rahoto cikin sauti daga Mahmud Ibrahim Kwari:

Dalilin Da Ya Sa Aka Rufe Babban Asibitin Khalifa Isiaku Rabiu A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


XS
SM
MD
LG