Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Baki Shiga Amurka Ta Fara Aiki


Kofar shiga wani filin tashin jirgen sama a Amurka
Kofar shiga wani filin tashin jirgen sama a Amurka

A yau Juma’a, Amurka ta fara aiwatar da sabbin dokokin hana baki shiga kasar ba tare da wata tangarda ba, ko wani rudani irin wanda aka samu a farkon kafa dokar ba.

Dokar ta fara aiki ne kwanaki kadan bayan da babbar kotun kolin Amurka ta amince da wani bangaren dokar Donald Trump ta fara aiki, bayan da wasu kananan kutuna suka dakatar da ita, da cewa ta sabawa kundin tsarin mulki.

Amurka ta fitar da sabbin dokoki a daren jiya Alhamis, dake bukatar masu neman visa daga wasu kasashe shida wadanda galibinsu na Musulmai ne, sai sun nuna shaidar cewa suna da alaka da wani ko wata dake zaune a Amurka, ko za su gudanar da kasuwanci ko wata harka ta aiki kafin a amince musu su shiga kasar.

A jiya Alhamis ne, hukumomin Amurka suka fitar da tsarin yadda ma’aikatun diplomasiyya za su tunkari sarrafa ba da tarkudun izinin neman shiga Amurka daga kasashen da suka hada da Iran da Libiya da Somalia da Sudan da Syria da kuma Yamal.

Duk wadanda aka riga aka amince masu shigowa Amurka daga wadannan kasashe kafin ranar 6 ga watan Yuli, za a bar su, su shiga ba tare da matsala ba, a cewar jami’an Amurka.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG