Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Mu Tallafawa Kananan Hukumomi-Gwamnan Jigawa


Gwamna Mohammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa, arewacin Najeriya

Yayin da kananan hukumomi a Najeriya suka fara karbar kason su na kudade aiwatar da ayyuka kai tsaye daga asusun tarayya a watan daya gabata na Yuni, gwamnonin jihohin sun janye tallafin da sukan yiwa kananan hukumomin.

Matakin da gwamnonin jihohin suka dauka ya sanya wasu daga cikin kananan hukumomin suka fara fuskantar kalubalen kudi, lamarin da ka iya haifar da koma baya ga ayyukan hukumomin su.

Amma gwamnan jihar Jigawa Badaru Abubakar yace tilas ne a fara tunanin matakan tallafawa kananan hukumomin har su tsaya da kafafun su kamar yadda gwamnatin tarayya ta agazawa wasu jihohi da suka tsinci kai a mawuyacin hali a shekarun baya.

Gwamnan yace a jiharsa ta Jigawa sun bi umarni kuma sun turawa kowace karamar hukuma rabonta ya kuma kyautata zaton babu wata karamar hukuma a jiharsa da zata huskanci wata gagarumar matsala.

Yace matsalar da aka samu a jihar Jigawa itace damuwa da ma’aikatan kananan hukumomi da na ilimin firamare suka nuna na rashin samun albashin su a ranar 25 ga wata amma a watan da ya gabata sai aka samu jinkiri saboda kudade daga Abuja basu shigo da wuri ba har sai ranar Laraba da ta shige kuma aka tura musu kudin a ranar Alhamis.

Gwamna Badau yace a baya kafin wannan umarni gwamnatin jiha ke ranta kudin biyan ma’aikatan kananan hukumomin su shigo kafin kudaden su su shigo. A dan haka yace zai dau mataki domin tabbatar da an bi tsari da zai bada daman rantawa kananan hukumomi kudi kafin su samu kudi daga tarayya.

Gwamnan Jigawa Abubakar Badaru ya yi wadannan kalamai ne a hirarsa da wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka a Kano Mahmud Ibrahim Kwari, ga kuma karin bayani:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00Facebook Forum

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG