Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Ne Jihohi Su Habaka Hanyoyin Samun Kudaden Shiga Na Cikin Gida -Osinbajo


Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo (Twitter/ Laolu Akande)
Mataimakin Shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo (Twitter/ Laolu Akande)

Mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi kira ga jihohi da su sake nazari mai zurfi, su kuma yi Tunani kamar kasashe masu 'yancin cin gashin kai, ta yadda za su bunkasa samun kudaden shiga na cikin gida domin tafiyar da lamurransu.

Farfesa Osinbajo ya yi wannan tsokaci ne a taron farko na dandalin saka hannun jari na jihar Ekiti da ya gudana a birnin Ado-Ekiti fadar gwamnatin jihar.

A cewar sa, kamata yayi gwamnonin jihohi su fara tunani na daban, a maimakon dogara da abinda suke samu daga gwamnatin tarayya, akwai bukatar su yi tunani kamar kasa mai cikakken iko don bunkasa hanyoyin samun kudadden shiga da zai taimaka wajen raya jihohinsu.

Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa wasu jihohin na da hanyoyin samun kudaden shiga na cikin gida masu kyau.

Haka kuma, Osinbajo ya ce wajibi ne jihohi su dauki nauyin wasu hakkokin da ke rataye a kan su, kamar biyan albashi daga kudaden shiga na cikin gida da su ke samu, wanda kuma zai rage musu dogaro kacokam kam gwamnatin tarayya.

Ya yi wa mahalarta taron tuni a kan yadda jihar Legas ta inganta samun kudadden shigarta na cikin gida wato IGR daga Naira miliyan 600 kowane wata a shekarar 1999 da 2000, zuwa kusan Naira biliyan 45 a yanzu.

Ya bayyana cewa kwace kadarorin da gwamnatin tarayya ta waccan lokacin ta yi ba bisa ka’ida ba, shi ne ya farga da jihar ta sake tunani kan habaka samun kudadenta.

To sai dai Farfesa Osinbajo ya lura cewa duk da cewa jiha ba kasa ba ce mai cin gashin kanta, amma ya zama dole ne ta yi hali irin na taraya a wajen samun kudadden shiga don kara bunkasa ci gaban tattalin arzikin ta.

A cewarsa, gwamnatin tarayya da na Jihohi za su iya cin gajiyar tattalin arzikin da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta, tare da lura da cewa tsarin da kamfanoni masu zaman kansu shine hanya madaidaiciya da za'a bi, kamar yadda yan kasa zasu iya cin moriyar tsarin kasuwanci na kamfanoni masu zaman kansu.

XS
SM
MD
LG