Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Mutunta Juna Tsakanin Ma'aurata-Kashi Na Daya-Nuwamba,05, 2020


Alheri Grace Abdu

Batun cin zarafin iyali wani lamari ne da yake faruwa ta fannoni daban daban wanda kuma yake iya shafar namiji ko mace, babba ko yaro. Galibin a tsakanin ma'aurata, mata suka fi fuskantar wannan matsala yayinda tsakanin 'ya'yan 'yan agola suka fi samun kansu a cikin wannan halin.

A cikin 'yan shekarun nan an sami yanayi inda wadansu dalilai suka sa ko dai iyaye su gallazawa 'ya'yan cikinsu ko kuma ma'aurata su ci zarafin abokan zamansu.

A yau shirin Domin Iyali ya gayyato wasu masu sa ido da kuma kula da lamura domin neman mafita. Bakin da shirin ya tattauna da su, su ne, Muhammad Hadi Musa mai ilimin halayyar dan adam kuma kwararre a fannin harkokin iyali, da Barrista Amina Umar Hussain sakatariyar kungiyar lauyoyi mata ta duniya reshen jihar Kano, da kuma Mal Abdulra'uf Magidanci kuma mai kula da lamura.

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Mutunta Juna Tsakanin Ma'aurata-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:24 0:00Saurari cikakkiyar tattaunawar da Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG