Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Bibiya Kan Kafa Dokar Dandaka A Jihar Kaduna-Kashi Na Daya, Satumba, 24, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Tun da aka fuskanci karuwar fyade a Najeriya, kungiyoyin kare hakkin bil'ama da kuma daidaitun jama'a suka shawarta sake salo da kuma hukumci mai tsanani da zai zama ishara ga masu aikata wannan cin zarafin, kama daga hukumcin kisa zuwa dandaka.

To gwamnatin jihar Kaduna ta shiga gaba a daukar wannan matakin inda ta kafa dokar dandake wanda aka samu da wannan laifin. Abinda shirin Domin Iyali ya nazarta ke nan a yau.

A cikin hirarsu da wakilinmu Isa Lawal Ikara. Kwamishinar ma'aikatar harkokin mata ta jihar Hajiya Hafsat Mohammed Baba, ta bayyana yadda suke kallon wannan doka da ta ce sun yi na'am da ita, ta kuma ce zasu bi ta sau da kafa domin ganin an yi wa wadanda ake zalunta adalci.

A nashi bayanin lauya mai zaman kansa, kuma mai bibiya kan lamura, El-Zibairu Abubakar ya bayyana matsalolin da yake gani zasu iya kadangaren bakin tulu dangane da wannan yunkuri .

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Kafa Dokar Dandaka A Jihar Kaduna-Kashi Na Daya-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:29 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG