Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Fyade a Garin Bauchi- Kashi Na Daya, Satumba, 17, 2020


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Makon jiya shirin Domin Iyali ya fara gabatar da batun mutumin nan dan shekaru 50 mai suna Yusuf Bako wanda aka kama yana yi wa wata karamar yarinya 'yar shekaru hudu fyade a masallaci.

Binciken 'yan sanda ya nuna mutumin ya yi zaman kurkuku har sau biyu sabili da samunsa da laifin fyade aka aka sake shi ya ci gaba da yawo a cikin al'umma.

Yau shirin Domin Iyali ya sami yin hira da Sheik Mu'azu Turkunya, limamin masallacin da mutumin ya aikata wannan abin takaici.

Saurari bayanin da limamin Masallacin ya yi mana a hirarshi da wakilinmu Abdulwahab Mohammad.

DOMIN IYALI: Bibiya Kan Fyade a Garin Bauchi Kashi Na Biyu-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:10 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG