Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Hira Da Mata Da Suka Tsaya Takarar Majalisun Jihohin Zamfara Da Katsina-Fabrairu, 16, 2023


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Duk da yake yunkurin mata da dama da su ka nemi tsayawa takara ya gamu da cikas a lokacin zabukan tsaida ‘yan takara, kalilan da suka haye wannan matakin na ganin idan aka zabe su, za su yi iyakar kokari domin ganin sun shawo kan matsaloli a da suka abbadabi iyali.

Shirin na yau, ya karbi bakuncin Hauwa Lawal ‘Yar Gata ‘yar takarar Majalisar dokoki a jihar Katsina, da kuma Sa’afatu Labo mai takara a jihar Zamfara, wadanda suka bayyana burin da su ke neman cimma da ya sa su ka tsaya takara, da kuma kalubale da su ke fuskanta.

Saurari tattaunawar da wakilin Sashen Hausa Sani Shu'aibu Malumfashi ya jagoranta:

DOMIN IYALI: Hira Da Mata Da Suka Tsaya Takarar Majalisun Jihohin Zamfara Da Katsina
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:11 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG