Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dubban 'Yan Kasashen Waje Dake Libya Sun Bar kasar


'Yan kasar Italiya suke sauka daga jirgin soja da ya kwaso su daga Libya.
'Yan kasar Italiya suke sauka daga jirgin soja da ya kwaso su daga Libya.

Dubban ‘yan kasashen waje dake Libya ne suka sami nasarar ficewa daga kasar,yayinda wasu kuma suka sami cikas a tashoshin sama da na ruwan Libya.

Dubban ‘yan kasashen waje dake Libya ne suka sami nasarar ficewa daga kasar,yayinda wasu kuma suka sami cikas a tashoshin sama da na ruwan Libya.

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta fidda sanarwa jiya Alhamis,tana gargadin ‘yan kasarta daker Libya sun hanzarta barin kasar.Haka kuma a wata snarwa ta daban Ma’aikatar tace jirgin fito d a ta yi shata domin jigilar Amurkawa da wasu ‘yan kasashen ketare har yanzu yana tashar ruwn Libya saboda munin yanayi.Wani kakaki yace akwai mutane 285 cikin jirgin,cikinsu da jami’an Amurka 40 da iyalansu,da wasu farar hula 127.

Jami’an Camnada sun bada labarin cewa kamfanin Inshorar wani kamfanin jiragen sama da zai dauki ‘yan kasar 105 ya soke inshoran jiragen saboda ganin kara tabarbarewar tsaro a Libya.

Ahalin yanzu kuma Britaniya ta kwashe wasu ‘yan kasarta jiya Alhamis,tana shirin kwasar wasu da jirgin yakinta na ruwa da yanzu haka yake tsaye a awata tasha a Bengazi.

Dubban wasun ‘yan kasashen waje har yanzu suna tashar jirage dake Tripoli,wasu kuma sun bi hanya zuwa Tunisia,da masar domin gudu daga tashe tashen hankula. Wani wakilin MA dake kan iyakar Libya da Masar daga gabashi yace mutane da dama suna ta tsallaka kan iyakar.Wata wakikliyar MA kuma dake kan matsallakar d a ake kira Ras El Jedir zuwa Tunisia tace taga ‘yan kasar Tunisia, Libya, Masar, da China da Turkawa suna tsallakawa.

XS
SM
MD
LG