Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Libiya na Zargin al-Ka'ida da 'Yan Kwaya a Tada Rikicin Kasarsa

Wasu 'yan Libiya kenen ke murnar yin nasara a zanga-zangarsu
Wasu 'yan Libiya kenen ke murnar yin nasara a zanga-zangarsu

Shugaban Libya Moammar Gadhafi yana zargin Osama bin Laden da kungiyar ‘yan ta’addar al-Qaida da laifin zama kanwa uwar gamin shirya zanga-zangar kin Gwamnatin da ake yi a kasarsa.

Shugaban Libya Moammar Gadhafi yana zargin Osama bin Laden da kungiyar ‘yan ta’addar al-Qaida da laifin zama kanwa uwar gamin shirya zanga-zangar kin Gwamnatin da ake yi a kasarsa.

Wani jawabin da yayi yau Alhamis, aka kuma yayata ta kafar Telbijin da wayoyin Tarho, anji yana cewa mayakan al-qaida ne suka rika baiwa matasan Libya kwaya suna sha domin gusar da hankulansu domin tada hargitsi da tawaye.Gadhafi yana mai cewa ba wanda ke cikin hankalinsa da zai rika abinda masu zanga-zangar keyi.

Ya kuma yi kira ga iyayen matasan Libya da su kokarta ladabtar da ‘ya’yansu, su kuma kirasu zuwa gida.

Babu wata kafar labarai mai zaman kanta data danganta zanga-zangar kasar Libya da kungiyar al-qaida. Gadhafi ya aike da sakon ta’zaiyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a dalilin tashe-tashen hankulan.

XS
SM
MD
LG