Wasu bayanai da suka shigowa ‘yan sanda a farkon watan nan na Janairu ne suka sanya hukumar OCRITIS mai yaki da fataucin miyagun kwaoyoyi ta kasar kaddamar da bincike wanda a karshe ya bada damar gano rukuni na farko na wasu ‘yan Nijer 3 dauke da kwayar Tramadol kimanin 4,000, wadanda suka fito da su daga jihar Kano da ke arewacin Najeriya
Sai rukuni na biyu na wasu mutane 7, su ma ‘yan Nijer ne da suka fito daga kasar Togo dauke da kwayar Tramadol sama da 100,000, kamar yadda mai magana da yawun hukumar ‘yan sandan Nijer Kwamishiniya Nana Aichatou Ousmane Bako ta yi wa manema labarai bayani a lokacin da aka gabatar da wadannan mutane.
Binciken ya yi nuni da cewa, gagarumin yaki da masu safarar miyagun kwayoyin da aka kaddamar a Jamhuriyar Nijer da makwafta ya haddasa karancin kwayar Tramadol a kasuwanni, lamarin da kuma ya janyo tsadarta a yanzu haka, shi ya sa suka fara neman hanyoyin samo kwayar ta Tramadol ruwa a jallo, inji mataimakiyar babban Alkali mai kare muradan hukumar Procureur de la Republique, Mme Maidamma Hadiza.
A ci gaba da karfafa matakan yaki da fatauci da shan miyagun kwayoyi, hukumar OCRTIS ta bude layin waya na musamman wanda jama’a za su iya kira don tsegunta wa jami’anta dukkan wani abinda ake zargin ya na da alaka ko ta’ammali da miyagun kwayoyi.
Hukumar ta OCRTIS ta kuma gargadi iyaye su kara maida hankali wajen tantance yanayin mutanen da ‘yayansu ke hulda da su a matsayin abokai ko kawaye.
Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma: