Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hadakar Jam'iyyun Kawancen PNDS Sun Jaddada Goyon Bayansu Ga Bazoum


Bazoum Mohamed

A jamhuriyar Nijar, yayin da ake tunkarar zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da za a yi a ranar 21 ga watan Fabrerun wannan shekarar ta 2021, jam’iyyun kawancen da suka mara wa dan takarar PNDS Bazoum Mohamed sun kara jaddada matsayinsu don ganin dan takarar ya lashe zaben.

A sanarwar da suka fitar ranar Litinin a cibiyar jam’iyyar PNDS Tarayya, shugabannin jam’iyyu 45 mambobin kawancen "Coalition Bazoum Mohamed 2021" sun jinjinawa magoya bayansu saboda yadda suka fito suka bai wa dan takarar wannan kawance kuri’un da suka bashi damar zuwa sahun gaba cikin ‘yan takara 30 da suka fafata a zagayen farko.

Bazoum Mohamed ya yaba da kokarin wadannan jam’iyyun duk kuwa da cewa ba a cimma gurin lashe zabe ba tun a zagayen farko kamar yadda aka yi fata.

Jam’iyyun na kawancen "Coalition Bazoum 2021" na ganin akwai alamun samun galaba a zagaye na biyu bisa la’akari da nasarorin da ‘yan takarar jam’iyyun kawancen da ke mulki suka samu a zagayen farko.

Bazoum Mohamed ya ce ya na da kwarin gwiwar samun hadin kan jam’iyyun kawancen na PNDS Tarayya.

Yanzu haka dai wasu majiyoyi na cewa tuni bangarorin ‘yan takarar da zasu kara a zaben zagaye na biyu na ranar 21 ga watan Fabreru suka fara tuntubar shugabannin jam’iyyun siyasa a bayan fage da nufin kulla kawance, a ci gaba da neman hanyoyin da zasu taimaka a kai ga lashe wannan zabe, yayin da masu amfani da kafafen sada zumunta ke ci gaba da tafka muhawara a game da yadda suke hasashen za ta kaya tsakanin tsohon ministan cikin gida Bazoum Mohamed da tsohon shugaban kasa Mahaman Ousman.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:23 0:00An Yi Jana’izar Idriss Deby Yayin Da Makomar Chadi Ke Cike Da Rashin Tabbas
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:38 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG