Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El Clasico - Real Madrid Ta Lallasa Barcelona 3:1


El Clasico.

Dazun nan aka kammala fafatawar jikakkiyar hamayya ta El Clasico inda Real Madrid ta lallasa Barcelona da ci uku da daya a yau Asabar a wasan La Liga na kasar Spain.

‘Yan wasan Madrid dai sun taka leda sosai kana sun mamaye baki dayan wasan musamman a zagaye na biyu.

Kwallo ta hanyar bugun panaliti da Real Madrid ta samu daga Sergio Ramos da kuma wani kwallon kusan karshen lokaci da Luka Modric ya zura ya sa kungiyar da Zinedine Zidane ke hoarswa ta yi galaba akan Barca da Ronald Koeman ke horas da ‘yan wasanta.

El Clasico
El Clasico

Fedrico Valverde ne ya fara zura kwallon farko a daidai minti biyar da fara wasan kana Barca ta maida martani bayan minti hudu da kwallon da Ansu Fati ya zura.

Lionel Messi
Lionel Messi

Lionel Messi ya samu dama da yawa na zura kwallo amma mai tsaron gidan Madri Thibaut Courtious ya yi ta doke su.

Facebook Forum

Ba Laifi Ba Ne Don Na Dawo Kano Pillars – Ahmed Musa
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:59 0:00
Karin bayani akan Diego Maradona

Gasar Premier League: Waye Zai Maye Gurbin Mourinho?

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG