Accessibility links

Rahotanni na cewa akalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu sananan dubbai suka tsere daga gidajensu dake kauyukan kan iyakar Kamaru da Nigeria domin kaucewa rikicin da ake tafkawa tsakanin makiyaya ‘yan Nigeria da Manoman kasar Kamaru.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewar Fulani makiyayan dake kokarin tserewa domin kaucewa rikicin da ake yi a kauyukan kan iyakar Nigeria ne suka fara maida martani cikin Fushi lokacin da Manoman kasar kamaru suka nemi tilasta masu sai lallai su bar kauyukan da suka je suka mamaye suna kiwon dabbobinsu.

Dan Majalisar dokokin kasar kamarun da muryar Amurka tayi hira dashi mai suna Walang Richard, ya shaidawa Muryar Amurka cewar Fulani ne suka fito da karfinsu baki daya dauke da makamai suka rika afkawa kauyukan ba zato ba tsammani, dan majalisa

Walang sai yayi Karin bayanin cewa "kai wadannan mutanen fa sun shirya yaki ne sosai, domin suna dauke da makamai, har ta kai suka fara kokkona ginin makarantu, suna bi suna rurrusa gidajen mutane, sun kuma shiga gonaki suna lalata kayan abinchin da aka noma, lallai abin bashi da kyawun gani."
XS
SM
MD
LG