Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Najeriya ta Maida Martani Akan Kudurin Hana Yada Labaran Bogi


Fadar ta shugaban Najeriya ta nesanta Shugaba Buhari da alhakin tura kudurin doka na rage ‘yancin yada labarai wanda ya sami karatu na biyu a gaban majalisar dattawan kasar.

Kakakin shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ya ce ba kai-tsaye shugaban ne ya tura kudurin ba, don a koda yaushe gwamnatinsa na goyon bayan ‘yancin kafafen sadarwa. Kudurin da ya fito daga hukumar kula da kafafen sadarwa ya taba samun adawa daga yawancin ‘yan Najeriya musamman a yanar gizo, dake ganin hanya ce ta takurawa manema labarai su kasa gudanar da aikinsu hakan kuma zai iya murkushe gaskiya.

“Duk labari, in dai zai kawo rudani, to ya kamata a kauce masa.” A cewar babban daraktan gidan talabijin din Najeriya na NTA Yakubu Muhammed. Ya kara da jan hankali akan cewa, bada labari, ko rahoto amana ne kuma dole ne labarin ya kasance gaskiya ba kirkirar labarin bogi ba, don aikin jarida babbar sana’a ce wadda zata iya yin gini, kuma za ta iya rusawa.

Sanata Na-Allah, a majalisar dattawan Najeriya ya kawo irin wannan kudurin a baya bayan cin zarafin da ya fuskanta a yanar gizo. Yanzu an zuba ido a ga ko wannan kudurin zai tsallake ko a’a.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG