Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

FILATO: Dakarun STF Sun Hallaka Wasu Yan Bindiga


Dakarun dake aikin wanzar da zaman lafiya a jahar Filato sunyi nasarar hallaka wasu masu garkuwa da mutane su uku, suka kuma kwace makamai.

Kakakin rundunar Tsaro ta Special Task Force a Jahar Filato, Manjo Ishaku Takwa ya ce tun a baya, jami’an tsaro na bibiyan gungun masu garkuwa da mutanen, wanda suke da tabbacin suna cikin wadanda suka fasa gidan yarin Jos, a watan Nuwamban bara.

A cikin kwanakin nan, jami’an tsaron na STF sun yi nasarar kwato mutane da aka yi garkuwa da su, ba tare da sun sami lahani ba.

Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong wanda ya yaba wa jami’an tsaron bisa kokarin nasu, ya kuma yi alkawarin sanya hannu don kisan duk wanda kotu ta tabbatar ya aikata laifin yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa.

XS
SM
MD
LG