Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Filato: Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Yari


Hukumar gidan gyara hali dake jahar Filato ta tabbatar da hari da ‘yan bindiga suka kai wa gidan yari.

A yammacin jiya Lahadi ne aka rika jin karar harbe-harbe a gidan yarin dake tsakiyar birnin Jos.

A wata sanarwa dake da sanya hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar gyara halin na kasa, Francis Enobore ta ce maharan sun zo da yawan gaske da muggan makamai suka bude wuta wa jami’an gidan yarin kafin suka balle babbar kofar gidan yarin suka shiga.

Sanarwar tace jami’an tsaro nan da nan suka kai martini cikin gaggawa, su ka killace, su ka kuma tsare kewayen gidan yarin kuma suna iya kokari su ga sun shawo kan lamarin, su kuma kama su.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:07 0:00


XS
SM
MD
LG