Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobara A India Ta Lakume Rayuka Goma Sha Bakwai


Gobara a India

A kalla mutane 17 sun mutu a yau Talata yayin da gobara ta tashi a cikin wani babban otal a birnin Delhi da sanyi safiya, wani sabon bala’I da ya haifar da damuwa a kan matakan tsare wuta a India.

Gobarar ta tashi ne a cikin wani otal mai suna Arpit Palace a wani bangare mai cike da jama’a a tsakiyar birnin Delhi, inda hotuna suka nuna yanda wutar take cinye ginin.

Mun tabbatar da wannan labarin tare da hukumomin asibitoci, da suka fada mana mutane 17 uka mutu ciki har da karamin yaro, inji Sunil Choudhary wani jami’in ‘yan kwana-kwana yana fadawa kamfanin dillancin labarai na AFP

Wasu kafafen labarai na cikin gida sun ce wata mace da danta sun mutu ne yayin da suka yi kokarin tserewa wutar suka tsallako a cikin taga.

Facebook Forum

Zauren VOA Hausa #EndSARS

Zauren VOA Hausa #EndSARS Kashi na Biyu 03
please wait

No media source currently available

0:00 0:18:31 0:00
Karin bayani akan #ENDSARS: Zanga Zangar Kyamar Gallazawa Al’umma Da Yan Sanda Ke Yi

Rayuwar Birni

Hira da Yusuf, wani dan asalin Jamhuriyar Nijar da ya shekara a Abuja yana sana’r gyaran takalmi
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:39 0:00
XS
SM
MD
LG